ABNA24 : Kamfanin dillancin labarai na “I-24-News ya bada labarin cewa wata mata da mijinta daga kasar UAE, wacce ta samar da huldar jakadanci da HKI a cikin watan Satumban da ya gabata, sun isa birnin tashar jiragen sama na Bengurio a birnin Telabiv da jirgin saman kamfanin “Fly Dubai”, amma aka hanasu shiga kasar.
Labarin ya kara da cewa daga karshe a dole suka koma kasarsu da jirgi mafi kusa da suka samu ba tare da shiga kasar ba.
Wasu majiyoyin jami’an tashar jiragen sam na yahudawan sun bayyana cewa an hanasu shiga kasar ne saboda takardun shigarsu basu da inganci.
Amma kafin haka yahudawan sahyoniyya da dama sun shiga kasar UAE ba tare da wata matsala ba.
A ranar 15 ga watan Satumban da ya gabata ne kasashen Bahrain da UAE suka kulla hurdar jakadanci da HKI duk tare da rashin amincewar Falasdinawa da mafi yawan mutane a kasashen na Larabawa.
342/